Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Tinubu Ya Nada Kemi Nandap A Matsayin Shugabar Hukumar Shige Da Fice


Shugaban Hukumar Shige da Fice, Kemi Nandap
Shugaban Hukumar Shige da Fice, Kemi Nandap

Shugaba Bola Tinubu ya nada Kemi Nanna Nandap a matsayin sabuwar Shugabar Hukumar Shige da fice ta Kasar Najeria.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, in da yace ''nadin zai fara aiki da ga 1 ga watan Maris na shekaar 2024''.

“DCG Nandap za ta maye gurbin Caroline Wura-Ola, wadda wa'adin ta a ofishin zai kare a ranar 29 ga watan Fabrairu da mu ke ciki”, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaba Tinubu na kyautata zaton ''sabuwar shugabar za ta karfafa tsaron ƙasa ta hanyar samar da ingantaccen tsaro a kan iyakokin ƙasa da kula da al’amuran baƙin haure'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kafin naɗa ta a matsayin Kwanturola-Janar, Nandap ce Mataimakiyar Kwanturolan-Janar mai kula da sashen hijira.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG