Ma'aikatar Shari'ar Amurka na bukatar Kotun Koli ta soke hukuncin wani alkalin kotun Tarayya, wanda ya tsame kakannin mutanen da ke zaune a Amurka, daga cikin jerin mutanen da dokar hana shigowa ta Shugaba Donald Trump ta shafa.
Ma'aikatar ta Shari'a ta gabatar da bukatar a gaggauce da daren jiya Jumma'a.
Ranar Alhamis wani alkalin kotun gunduma a Honolulu mai suna Derrick Watson ya yi kiran da a rinka amfani da abinda ya kira "hankali" yayin da ya ke kara nau'ukan 'yan uwan mutanen da ke zauna a Amurka da ka iya shigowa daga kasashe 6 masu rinjayen Musulmi - wato Iran da Libiya da Somaliya da Sudan da Siriya da Yemen.
Watson ya umurci gwamnati da kar ta aiwatar da dokar kan kakanni, da jikoki da kuma surukai da goggonni da kawunnan mutanen da ke zaune a Amurka.
Watson ya kuma zartas cewa duk wani dan gudun hijirar da wata cibiyar tsugunar da 'yan gudun hijira ta yi alkawarin daukar nauyinsa a Amurka a bar shi ya shigo.