Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sanda Tayi Alkawarin Adalci A Rikicin Direbobi Da FRSC A Jigawa


 Shugaban 'yan sandan Najeriya
Shugaban 'yan sandan Najeriya

Hankalin ya kwanta biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin direbobi da jami'an hukumar kare hatsari na Najeriya.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Jigawa Rasheed Olatunde Akintunde, ya gana da masu ruwa da tsaki akan harkar sifiri a jihar jigawa.

Wannan ganawa ta biyo bayan barkewar wani rikici a jihar tsakanin direbobi da hukumar kiyaye haddura na Najeriya watau “Federal Road Safety Corp”.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan, na jihar ta Jigawa SP Abdul Jinjiri, ya bayana haka a wata hira da wakilin muryar Amurka Mahnmud Ibrahim Kwari.

Ya kara da cewa rundunar zata tabbatar da ganin cewa ta gudanar da bincike na gaskiya domin gano musabbabin afkuwar wannan rikici wanda har yayi sanadiyar mutuwar wani direba da kuma harbin wani dan Sanda.

Ya na mai cewa kawo yanzu dai komai ya lafa a jihar kuma kwamishinan ‘yan Sandan ya gana da ‘yan uwan wanda ya rasa rainsa a sakamakon wanna rikici inda ya basu tabbaci tabbatar da adalci a binciken.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG