Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Matashi Mai Alaka Da Hare-Haren Ruwan Sinadari Mai Guba a London


Emergency response following acid attack on the junction of Hackney Road with Queensbridge Road, London, July 13, 2017.
Emergency response following acid attack on the junction of Hackney Road with Queensbridge Road, London, July 13, 2017.

Biyo bayan hare-haren ruwan sinadari mai guba da aka kai kan wasu mutane a birnin London, an kama wani matashi da ake zargi da hannu a hare-haren.

A yau Juma’a ‘yan sanda a birnin London suka ce an kama wani matashi dake alaka da hare-haren da aka sha kaiwa da ruwan sinadari mai guba, da ya kona fukokin mutane masu yawa a gabashin London.

‘Daya daga cikin mutanen da wannan lamari ya rustsa da su na cikin mawuyacin hali a cewar ‘yan sandan.

Kamar yadda jami’ai suka tabbatar, wasu mutane biyu sun jefa ruwan sinadarin gubar kan wani mutum mai shekaru 32 da haihuwa, suka kuma sace masa babur ‘dinsa kafin su ci gaba da gudanar da ire-iren harin kan sauran al’umma har na tsawon mintuna 90 a jiya Alhamis.

An dai kame matashin mai shekaru 16 da zargin fashi da makami da kuma laifin lalatawa jikkata mutum, a cewar ‘yan sandan, suna kuma neman karin bayani ga jama’a.

Wannan hari dai yazo ne bayan wasu hare-haren da aka kai London, ciki har da batun da aka zargi wani mutum da jefa wasu lalatattun abu kan wata fitattaciya da ‘yar uwarta alokacin da suke cikin mota.

Kwamishinan ‘yan sandan London, Cressida Dick, ya ce duk da yek ire-iren wannan hare-hare na karuwa amma har yanzu abu ne da aka saba gani ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG