Alkalan dai sun fara yajin aiki tun ranar 1 ga watan Mayu, suna bukatar shugaba Kiir ya yi musu karin albashi, ya kuma aiwatar da wasu sauye-sauye a fannin aikinsu, ya kuma cire shugaban alkalai Chan Reec Madut daga aikinsa saboda watsin da yayi da bukatun na su.
A wani taron manema labarai da aka yi a birnin Juba, Bold Lul Wang, mai wakiltar alkalan na Sudan ta Kudu, ya ce Alkalan sunyi matukar tabuwa da jin abin da Kiir yayi, na yin amfani da ikonsa na shugaban kasa ya kafa doka ranar Laraba.
Wang ya ce Alkalan Sudan ta Kudu sun gudanar da wani taron gaggawa yau Juma’a a Juba da sauran garuruwa a fadin kasar domin tattaunawa kan korar da aka yiwa wasu alkalai.
Alkalan dai na kira ga shugaban kasar cikin gaggawa da ya dawo da wadanda ya kora, ya kuma biya musu bukatun da suke nema. Ya kuma ce baki ‘daya alkalan suna goyon bayan ‘yan uwansu da aka kora.
Facebook Forum