Shugaban Amurka Donald Trump shine babban bako a bikin cika shekaru 100 da Amurka ta shiga yakin Duniya, inda sojojin Faransa suka gudanar da shagulgula da suka hada da kade-kade da wasanni da jiragen saman yaki masu shawagi a acikin sararin samaniya, bukin dai ya kwashe sama da sa’o’i biyu ana gudanar da shi.
Tutocin Amurka da na Faransa sunyi ta kadawa a zagayen sanannan dandalin nan na Champs Elysees, inda dakarun Amurka suka yi maci tare da dubban dakarun Faransa, dauke da kayayyakin yaki irinsu tankoki da makamai masu linzami.
Sama da ‘yan sanda 3,500 suka mamaye wajen bukin domin samar da tsaro da dakile yiwuwar harin ta’addanci.
Wannan biki da aka gudanar a Faransa yazo ne shekara guda bayan da wata babbar mota ta kai hari ta kashe mutane 86 a birnin Nice, harin da kungiyar ISIS ta ‘dauki alhakin kai shi.
Da suke sallama a yau Juma’a, shugaba Trump da shugaba Emmanuel Macron da matarsa Brigitte, sunyi tafiya tare kafin Macron ya jinjina hannun Trump na wasu ‘yan dakikoki, wanda hakan ya zama wata al’ada ga shugabannin biyu
Facebook Forum