Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Yin Gyara a Dokar Trump Ta Hana Wasu Baki Shigowa Amurka


Wani Alkalin Amurka yayi kira ga hukumomi da su rinka amfani da basira da hankali wajen zartar da manufofinsu.

Alkalin yana wannan kiran ne alokcin da yake kara yawan jerin mutanen da ya kamata a rinka baiwa damar ziyartar ‘yan uwansu dake Amurka daga kasashe shida da yawancinsu musulmai ne wadanda gwamnatin shugaba Donald Trump ke kokarin hanawa ‘yan kasashensu zuwa Amurka.

Cikin dokar da Trump ya samar an haramtawa kakanni da ‘yan uwa na nesa su ziyarci ‘dan uwa ko ‘yar uwarsu dake zaune a Amurka.

Amurka dai ta saka wannan doka ne kan mutanen da suka fito daga kasashen Iran da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yamal.

A jiya Alhamis ne alkalin kotun da ke birnin Honolulu, Derrick Watson, ya umarci gwamnatin Amurka da kada ta tayi amfani da dokar wajen hana kakanni da jikoki da mutanen da aure ya hada su da ‘yan uwan mazauna Amurka da kuma kannen iyaye ko yayu da ‘yar‘uwa ko dan uwa ko ‘da.

A watan Yuni ne kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa za a iya soma amfani da wasu sassa na wannan dokar a yanzu kafin ayi cikakken zaman kotu kan yanke hukunci a kan dokar baki dayanta kafin karshen shekarar nan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG