NIAMEY, NIGER - Wannan yunkurin na ma’aikatar kudin hanya ce ta samar da daidaito a tsakanin adadin ma’aikata da kudaden albashin da ake kashewa a kowane wata.
Matakin da kungiyoyin kwadago su ka yaba da shi, koda yake sun bayyana fatan ganin a wannan karo komai zai kammalu don ganin an hada cikakken kundin rajistar ma’aikata.
A shekarar 2019 ne hukumomin Nijar suka kaddamar da ayyukan rajistar ma’aikatan gwamnati da zummar tantance ma’aikata na gaskiya da na bogi ta yadda za a kawo karshen cuwa-cuwar da ake hasashen ta yi kamari a ma’aikatun kasar.
Bayan shafe shekaru sama da kididdiga kwamitin da aka damka wa wannan aiki ya fitar da sakamakon wucin gadi na abubuwan da ya gano.
Oumarou Barmou, wanda shi ne sakataren kungiyar jami’an ma’aikatar kudi ta kasa, ya ce binciken a wani bangaren ya lura da wasu ma’aikatan da bayanai ke nuna suna cikin yanayi mai cike da hazo, saboda haka aka dibar masu wa’adi domin su gabatar da hujjojin da ke nuna cewa ba su shigo ta bayan gida ba.
Sakataren uwar kungiyoyin kwadago ta CDTN Malan Ibro Kane wanda ke ganin dacewar bullo da wannan tsari na hada kundin rajistar ma’aikata mai zanen yatsu ya kalubalanci yanayin tafiyar wannan aiki.
An jima mahukuntan Nijar na kwatanta irin wannan yunkuri na kididdige ma’aikata sai dai abin baya tafiya daidai saboda wasu dalilai, abin da ya sa Oumarou Barmou ke jan hankulan gwamnatin kasar ta dage don ganin haka ta cimma ruwa a wannan karon.
Kawo yanzu ba a bayar da wasu alkaluma ba game da adadin ma’akatan da aka yi wa rajista, sai dai wata majiya na cewa a karshen ayyukan ne kwamitin zai fayyace wa jama’a yawan ma’aikatan da sunayensu za su bayyana a kammalallen kundin rajistar ma’aikata mai zanen yatsu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5