Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Maniyata Daga Nijer Sun Fara Fidda Ran Samun Sauke Farali A Bana


Jirgin saman Boeing 747-8
Jirgin saman Boeing 747-8

A jamhuriyar Nijer wasu daga cikin maniyatan aikin Hajji sun fara komawa garuruwansu bayan la’akari da cewa zai yi wuya a kai su kasar Saudiya kafin ranar 6 ga watan Yuli, duk da cewa mahukuntan Nijer sun sha alwashin kwashe dukkan mutanen da suka samu takardar Visa.

NIAMEY, NIGER - Malam Mansour Ousman, mazaunin birnin Cotonou a jamhuriyar Benin ne, tun a shekarar 2020 ya yi rajista a Nijer da nufin zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali, sai dai bayan shafe makonni biyu a birnin Yamai ya na jiran jirgi ya gano cewa wannan tafiya ba za ta yiwu ba a bana.

Shi ma Mikha’il wanda ya yi sha’awar zuwa Saudiya daga Nijer a maimakon ya yi rajista a jamhuriyar Benin inda ya ke zaune, ya tsinci kansa cikin irin wannan hali.

A tsakiyar makon jiya ne gwamnatin Nijer a ta bakin kakakinta Tidjani Abdoulkadri ta bada tabbacin daukar dukkan matakan ganin kowane daga cikin maniyata 7,194 da suka yi rajista sun isa kasar Saudiya kafin shudewar wa’adin ranar 6 ga watan Yuli, sai dai rashin zuwan babban jirgin Boeing 747 da aka yi hasashen zai fara kwashe mutun sama da 500 a duk sawu daya ya sa aka fara shakka, abinda ya sa wasu maniyatan suka fara tunanin komawa gida don rungumar kaddara.

Bayanai daga sashen kula da harkokin sadarwa a hukumar alhazai ta kasa ta COHO na cewa daga cikin maniyata 7,194 da suka yi rajista 5,107 sun samu tafiya yayin da ake ci gaba da fafutikar ganin sauran maniyata 2,087 da suka rage sun shiga Saudiya tun wuri bai kure ba.

Matsalolin aiyukan Hajji a Nijer wani laifi ne da ake dora alhakinsa a kan ejojin kamfanonin Hajji da Umara saboda yadda wasu daga cikinsu suka mayar da abin kasuwanci kuma a dayan gefen ana zargin hukumar alhazai ta COHO da rashin sanin makamar aiki kamar yadda abin ke shafar kamfanonin shatar jiragen jigilar maniyata.

Saurari rahoton Souley Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG