Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Takaddama Kan Ranar Da Ya Kamata A Yi Babbar Sallah A Nijar


 Shugaban Nijar Mohamed Bazoum lokacin Sallar Idi 2021 a birnin Yamai
 Shugaban Nijar Mohamed Bazoum lokacin Sallar Idi 2021 a birnin Yamai

A Jamhuriyar Nijar an shiga halin dambarwa bayan da majalisar addinin Islama a kasar ta ayyana ranar Lahadi 10 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a yi bukukwan babbar sallar a maimakon ranar asabar.

NIAMEY, NIGER - Kiraye-kirayen da jama’ar ta yi akan wannan batu ya tilasata wa majalissar canza matsayi, ta na mai cewa kuskure ne aka yi.

A sanarwar da suka bayar ta kafafen yada labaran gwamnatin Nijar, shugabanin majalisar malamai ta addinin Isalama wato Conseil Islamique sun ce sun cika daren Laraba 29 ga watan Yuni suna sa ido don samun labarin ganin jaririn wata sai dai shiru babu, abin da ke nufin ba garin da aka hango jaririn wata a duk fadin Nijar.

Kakakin majalisar ta malamai Cheik Abdourahamane Amadou a wannan sanarwa ya ci gaba da cewa kasancewar watan musulunci bai taba wuce kwanaki 30 ba saboda haka ranar Juma’a ita ce ranar 1 ga watan Zul hijja kenan za a yi Idin Sallar Layya a ranar Lahadi 10 ga watan Yulin 2022 dake dai dai da ranar 10 ga watan Zul Hijjan shekarar Hijira ta 1443.

Sai dai wannan sanarwa ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, kuma wadanda muka tuntuba da wannan batu na cewa akwai kuskure a lissafin na majalissar malamai.

Sai dai majalisar ta canza matsayi bayan da a ranar Alhamis aka ga watan Zul Hijja a birnin Yamai da wasu garuruwan kasar wanda har kusan karfe 9 na dare bai bace ba.

A dokar Nijar majalissar malaman addinin Islama ce ke da hurumin kula da sha’anin tabbatar da ganin wata ko akasin haka, sannan ita ke ayyana ranar da ya kamata a yi Sallar Idi, kasancewarta mai bai wa hukumomin kasar shawarwari akan addinin Musulunci.

Sai dai abin lura a ‘yan shekarun nan kurakuren da ke tattare da tafiyar ayyukanta na haifar da rudani kamar yadda abin ya wakana a watan Ramadan din da ya gabata, inda majalisar ta ba da sanarwar cewa ba a ga jaririn wata ba, kuma a tsakiyar dare ta kuma sake fitar da sanarwar ganin watan a wani lokacin da mutane da dama suka shiga barci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Ana Takaddama Kan Ranar Da Ya Kamata A Yi Babbar Sallah A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG