Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Ta'addanci: Aljeriya Da Nijer Za Su Hada Kai


Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer da Shugaba Abdulmajid Tebboune
Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer da Shugaba Abdulmajid Tebboune

Yayin da kasashen Aljeriya da Nijer ke fama da matsalolin ta'addanci da rashin ingantaccen tsarin sufuri, kasashen biyu na duba yiwuwar hada kai wajen magance matsalolin.

Aljeriya da Jumhuriyar Niger sun amince su duba yiwuwar kyautata harkar sufuri da yaki da ta'adanci da kuma batun da ya shafi 'yan cirani dake kwarara zuwa kasar Aljeriya a tsakaninsu ta yadda harkokin kasuwanci da tattalin arzikinsu za su bunkasa.

Kasashen biyun sun kuduri wannan aniyar ce a wata tattaunawar da shugabannin kasashen biyu suka yi, lokacin wata ziyarar da shugaban Jumhuriyar Niger, Mohamed Bazoum ya kai. Jama'a a jihar Agadez na fatan wannnan karon ziyarar ta kasance ta samun maganin matsalolin da fannin kasuwanci ke dasu, ba ziyara irin wacce shugaban na Nijar ya kai shekarar da ta wuce ba.

Kasashen biyu sun kuduri aniyar ce a wata tattaunawa da shugabanninsu su ka yi lokacin wata ziyara da shugaban Nijar bazoum Mohamed yakai kasar Aljeriya. Shugabannin biyu wato Abdulmajid Tebboune da Mohamed Bazoum na Nijar sun amince su bunkasa tattalin arzikinsu da yaki da taadanci da kuma dakile kwararar 'yan cirani zuwa kasar Aljeriya

kasar Aljeriya, tun asali, ta na da kima a idanun al’ummar Nijar, sakamakon manyan tsare tsaren da kasar ta samar a Nijar. Ziyarar da ke zama ta biyu da shugaban na Nijar ya kai a Aljeriya tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Nijar tuni dai al’ummar ta Nijar su ka fara bayyana ra'ayoyinsu kan wannan ziyarar ta shugaba Bazoum Mohamed tare da yadda suke fatan ziyarar ta kasance.

Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer da mai masaukinsa na shan fareti a filin jirgin sama a Aljeriya.
Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer da mai masaukinsa na shan fareti a filin jirgin sama a Aljeriya.

Shi dai Aminu Waje, wanda shi ne shugaban 'yan kasuwa na Agades ya nuna cewa ganin yadda har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba dangane da irin kudirorin da suke amincewa da su a can baya ya kyautu shugaban na Nijar da mai masaukinsa su sake nazarin wannan batun.

Alkasum Mato, masanin tattalin arziki, ya bayyana cewa akwai haske cikin wannan ziyarar ta yadda Nijar za ta rika shigar da kayanta kasar Aljeriya ita ma ta shigo da nata Nijar sai kuma gwamnatin Nijar ta yi kokarin hana 'yan cirani zuwa kasar.

Saukar Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer
Saukar Shugaba Bazoum Mohamed na Nijer

A halin yanzu dai kallo ya koma ga yadda huldar kasar Nijar da Aljeriya zata kasance anan gaba, ganin yadda shugaban na Nijar Bazoum Mohamed ke son kawo sauye sauye masu tarin yawa ta yadda 'yan kasa za su rinka gani a kasa aduk wata hulda da zai yi tsakanin kasa da kasa, musamman kasar Aljeriya da ke zama babbar kawa ga kasar Nijar.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG