Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Diffa Na Zargin Hukumomi Da Nuna Fifiko Ga Tubabbun ‘Yan Boko Haram


Bazoum shugaban Nijer
Bazoum shugaban Nijer

A jihar Diffa ta Jamhuriyyar Nijar, matasan jihar sun koka da cewa, hukumomin jihar da kungiyoyin bayar da tallafi sun manta da su, abin da ya fi daukar hankalinsu a yanzu shi ne tallafawa tubabbun ‘yan Boko Haram.

DIFFA, NIGER - Mutanen Jihar a nasu bangaren suna ci gaba da zaman jiran gawon shanu domin samun tallafi na dogara da kai, bayan da rikicin Boko Haram ya raba su da ayyukansu.

Wadannan su ne irin korafe-korafen da matasan na jihar Diffa ke ci gaba da yi, bayan shekaru da dama da da yawa daga cikinsu suka rasa ayyukansu sakamakon rikicin Boko Haram.

A baya dai akasarin matasan na jihar Diffa sun dogara ne da noma da kiwo da kuma kamun kifi, amma sakamakon dokar ta baci da hukumomin Nijar suka sakawa jihar bayan da rikicin na Boko Haram ya yi kamari a shekarar 2015, hakan ya tilassawa matasan jihar barin wadannan ayyukan.

Matasan na jihar Diffa na kalubalantar yadda hukumomin jihar da kuma kungiyoyin bayar da tallafi suka fi bayar da fifiko ga tallafawa tubabbun ‘yan Boko Haram, ba tare da al’akari da cewa suma suna bukatar wannan tallafin ba.

Binciki dai ya nuna cewa, daga farkon wannan shekarar ta 2022 kawo yanzu, kimanin matsan jihar Diffa dubu uku suka yi rajista neman aikin yi a ma’akatar dake kula da samar da aiki ta jihar Diffa.

Sai dai Kolo Mamadou, wanda shi ne mataimakin magajin garin jihar Diffa ya musanta wannan zargi da matasan suke yi, yana mai cewa damuwar matasa na daga cikin batutuwan da suka sa a gaba a yankin.

Babban abin da ya fi daukar hankalin Gawamnatin Nijar a yanzu shi ne batun maido da zaman lafiya a duk fadin jihar ta Diffa, inda a ranar Asabar shugaban kasar Mohamed Bazoum zai sake kai ziyara a jihar ta Diffa a karo na biyu, tun bayan hawansa kan garagar mulki, wanda zai gana da jami’an tsaro dake kokarin wanzar da zaman lafiya a jihar da hukumomin jihar da ma al’umma.

XS
SM
MD
LG