AGADEZ, NIGER - An kammala taron zaman lafiya da shugaban Nijar Mohammed Bazoum ya jagoranta a jihar Agadas bayan ya saurari bayanai da shawarwari daga dukkan bangarorin al’umma da suka bayar domin samo musu mafita.
Shugaban na Nijar ya bai wa ‘yan bindiga dama ta karshe da su ajiye makamansu ko kuma su fuskanci fushin gwamnati, ya kuma yi alkawarin taimaka wa kasashen yankin Sahel domin lalubo hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.
“Mun bai wa wadannan bata garin dama ta karshe domin su tuba su mika wuya. Ba zamu zuba musu ido muna kallo suna kwace dukiyoyin jama’a ba wani lokacin har ta kai ga salwantar da rayukansu," a cewar Bazoum.
Ya kara da cewa "zamu karfafa duk wasu matakai na bin diddigin samun bayanai na sirri domin mu yaki wannan annoba, kuma mun tattara bayanai kan batun safarar makaman da ake bi da su ta hamadar Sahara, a saboda haka muna jan kunnensu tare da yin kira ga matasan da suka yi nisa a fashi da makami da ma safarar miyagun kwayoyi da su daina."
Tuni dai kwamitin zaman lafiya na jihar Agadas ya yaba da matakin shugaban duba da cewa Agadas jiha ce a duk fadin kasar Nijar da ta fi sanin illar rashin zaman lafiya.
Alham Bubakar, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya jaddada gargadin da shugaban na Nijar ya yi ya kuma ce idan 'yan bindigar ba su ji gargadin ba to suna iya fuskantar hukuncin dauri a gidan kaso.
A nasu bangaren 'yan jihar Agadas sun yi fatan samun maganin matsalolin ‘yan bindiga cikin gaggawa.
Saurari rahoton Hamid Mahmud: