Ma’aikatar Cikin Gidan Nijar Ta Hana Hukumar UNDP Gudanar Da Rangadi A Jihohin Kasar

UNDP

Ma’aikatar cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta hana wani rangadin da hukumar UNDP ta kudiri aniyar gudanarwa a jihohin kasar da nufin bitar yanayin tsaron da ake ciki, wanda ba a bayyana dalilan daukan wannan mataki ba.

Tuni ‘yan kasa suka fara bayyana ra’ayoyi akan wannan al’amari. A yayin da wasu ke cewa hakan ya yi daidai wasun kuwa na ganin an tafka kuskure.

Ta hanyar wata takardar sakon da aka aike wa gwamnonin jihohi ne ministan cikin gidan Nijar ya sanar da su cewa ma’aikatarsa ta hana zagayen da hukumar majalissar dinkin duniya mai kula da raya karkara UNDP ko PNUD ke shirin gudanarwa a jihohi don bitar yanayin da sha’anin tsaro ke ciki a kasar.

Ba a dai fayyace dalilin hana gudanar da wannan rangadi ba, to amma tuni ‘yan kasa suka fara bayyana matsayinsu akan batun.

Haka ma’aikatar cikin gidan ta umurci gwamnonin jihohi su dauki dukkan matakan da suka dace don ganin an yi biyayya wa wannan mataki, amma kuma shugaban kungiyar FCR Souley Oumarou na ganin bukatar a duba batun.

Tantance abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum wani bangare na ayyuka da tun fil azal hukumar UNDP ko PNUD ke gudanarwa a karkashin MDD don samar da alkaluman kididdiga na zahirin yanayin walwalar jama’a a kowace kasa inji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum.

Wannan mataki dai na hana hukumar UNDP ko PNUD gudanar da zagayen da ta kudiri aniyar yi don tantance halin da fannin tsaro ke ciki a sassan Nijar na zuwa ne a wani lokacin da ma’aikatar cikin gida ta haramta wa kungiyoyi masu zaman kansu na gida da waje kai ziyara a gidajen yari a yayin da wani matakin na daban ke zama umurni ga kungiyoyi cewa nan gaba dole ne su sanar da ma’aikatar cikin gida kafin su gayyaci sarakuna zuwa wani taron da suka tsara.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ma’aikatar Cikin Gidan Nijar Ta Hana Hukumar UNDP Gudanar Da Rangadi A Jihohin Kasar