Firai Ministan, da ya isa kasar a jiya litinin da dare, ya jagorancin tawagar jami’an gwamnatin da suka hada da Ministan Tsaron Kasa da na Kasuwanci da na Man Fetur da na Noma da na Matasa.
Masani a sha’anin diplomasiya, Moustapha Abdoulaye, na fassara wannan rangadi a matsayin matakin neman hanyoyin cike gibin da dambarwar juyin mulkin 26 ga watan yulin 2023 ta haifar.
Ta wani bangare rangadin hanya ce ta laluben matakan magance radadin takunkumin da kungiyar CEDEAO ta saka wa kasar ta Nijar akalla watanni 6 da suka gabata.
Iran da Turkiya da Serbia na daga cikin jerin kasashen da gwamnatin rikon kwaryar Nijar ke fatan karfafa hulda da su a dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da matsalolin tsaro kwatankwacin yadda abin yake a wajen kawayenta Mali da Burkina Faso wadanda tun tuni suke da huldar aiyukan tsaro da kasar Rasha. Hakan ya sa ake ganin ba mamaki Nijar ma ta bi sahu.
A farkon watan disamban 2023 Karamin Ministan Tsaron Rasha, Yunus Bek Yevkurov, ya ziyarci Nijar inda suka tattauna da Shugaban majalissar CNSP Janar Tiani da Ministan Tsaro da takwaransa na Cikin Gida inda kasahen 2 suka cimma yarjejeniya kan harkokin tsaro musamman batun horon jami’an tsaro.
Ga cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna