Ana saran wata tawagar ta daban za ta isa kasar Nijar a makon gobe, domin tabbatar da cewa an yi komai cikin haske da daraja juna a tsakanin bangarorin biyu.
Sai dai kawo yanzu ba wata sanarwa daga bangaren Nijar akan wannan shiri.
Sanarwar da ofishin kakakin gwamnatin Amurka ya fitar a yammacin ranar Laraba, na cewa jakadiyar Amurka a Nijar, Kathleen Fitzgbbon da darektan dubarun aiki da tsare tsare a rundunar sojan Amurka, mai sansanin a nahiyar Afrika, Janar Ken Ekman, na ganawa da shugabanin Majalissar CNSP a ranar Alhamis 25 ga watan Afrilu a birnin Yamai, domin tattauna tsarin da zai kai ga kwashe dakarun Amurka.
Malan Sabo Saidou wani fitaccen dan siyasa da ya taka rawa a shirin mayar da Nijar kan tafarkin dimokradiya a farkon shekarun 1990 ya yaba da wannan yunkuri.
A makon gobe mataimakin sakataren tsaron Amurka mai kula da aiyukan musamman, Christopher Maier, da darektan ci gaban rundunonin sojan Amurka, Laftana Janar Dag Anderson za su ziyarci birnin Yamai, domin halartar wani taron, a cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa Amurka na alfahari da huldar fannin tsaro da irin sadaukarwar hadin gwiwar sojojinta da na Nijar a bisa la’akari da nasarorin da alakar kasashen biyu ta samar wajen wanzar da zaman lafiya a Nijar da ma wannan yanki baki daya.
Masani kan huldar kasa da kasa, Moustapha Abdoulaye, na cewa difloamsiya ta yi tasiri a wannan sha’ani.
Rashin cimma daidaito da Majalissar CNSP dangane da batun zaman sojinta a Nijar ne ya sa Amurka yanke shawarar bada kai bori ya hau yayin da ake sa ran mataimakin sakataren Amurkar, Kurt Campbell, zai yi rangadi a Nijar a watannin da ke tafe a cewar wannan sanarwa.
A ranar 16 ga watan Maris na 2024 ne gwamnatin rikon kwaryar Nijar ta bada sanarwar yanke huldar aiyukan soja da Amurka, sakamakon abin da ta kira soke halaccin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma a 2012 da sunan yaki da ta’addanci.
Kasa da wata guda bayan daukan wannan mataki Nijar din ta sanar da isowar wasu makaman kare sararin samaniya daga Rasha, hade da wasu dakarunta kimanin 100 masu aikin horo a ci gaba da fadada huldarta da manyan kasashen duniya.
Domin karin bayani saurari rahotan Souley Moumouni Barma.
Dandalin Mu Tattauna