Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Jami'an Gwamnatin Amurka Da Ta Kai Ziyara Nijar Ta Fara Tattauna Kan Komawa Dimokradiya


Tawagar Amurka da ta kai ziyara Nijar
Tawagar Amurka da ta kai ziyara Nijar

Wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Amurka da ke ziyara a jamhuriyar Nijar na ci gaba da tattaunawa da hukumomin rikon kwayar kasar a wuni na uku domin jin inda aka kwana game da tsare-tsaren jadawalin gudanar da al’amuran mulkin rikon kwarya.

NIAMEY, NIGER - Sun kuma tattauna akan zabubuka da hanyoyin da za su bada damar mayar da ragamar mulki ga hannun farar hula.

Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya tarbi tawagar Amurka da ta kai ziyara
Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya tarbi tawagar Amurka da ta kai ziyara

Koda yake tawwagar ba ta sami ganawa da Shugaban Majalissar CNSP Janar Tiani ba, masu fashin baki kan siyasar kasar na cewa yunkurin gwamnatin ta Amurka na da mahimmanci sosai.

Tawwagar wacce ta kunshi Mataimakiyar Sakataren Gwamnatin Amurka mai kula da harakokin Afrika Molly, Phee da Mataimakin Sakataren Gwamnatin Amurka mai kula da harakokin tsaron kasa da kasa, Celeste Wallander da kwamandan rundunar AFRICOM, Janar Michael Langley ta gana a wunin farko da Firaminista Ali Lamine Zeine da wasu mukarraban gwamnatin rikon kwarya da suka hada da Ministan tsaron kasa da na cikin gida da na harkokin waje da nufin tantance inda aka kwana game da shirin mayar da Nijar kan tafarkin dimokradiya.

Molly Phee mataimakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harkokin tsaron kasa da kasa ta na gaisawa da Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine
Molly Phee mataimakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harkokin tsaron kasa da kasa ta na gaisawa da Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine

Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum na fassara wannan ziyara da abin da ya kira mai mahimmancin gaske.

A cewar wani dan jarida kuma jami’i a cibiyar nazari da bincike ta CIRES Dr. Abba Seidik salon takun Amurka a rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin na Nijar alama ce da ke nunin girman kullin da ke tattare da wannan al’amari.

Molly Phee sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harkokin tsaron kasa da kasa
Molly Phee sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harkokin tsaron kasa da kasa

Kasar Amurka mai dakaru 1100 dake girke a yankin Agadez na horar da sojojin Nijar akan dubarun yaki da ta’addanci tare da samar da bayanan sirri kafin abubuwa su tsaya sanadiyar juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

A ziyarar da ta gudanar a watan Disamban da ya gabata Molly Phee ta nanata wa hukumomin rikon kwarya matsayin Amurka dangane da yi wa dimokradiya karan tsaye.

Yunkurin ganawa a tsakanin tawwagar ta Amurka da Janar Abdourahamane Tiani a ranar 13 ga watan Maris wato ranar Laraba dai ta ci tura a cewar wata majiya, koda yake ba a bayyana dalilan faruwar hakan ba sai dai a wannan Alhamis 14 ga watan Maris ma an sake wani zama na biyu a tsakanin Firaminista da jami’an gwamnatin ta Amurka.

Lokacin da tawagar Amurka ke ganawa ta wasu shugabannin Nijar
Lokacin da tawagar Amurka ke ganawa ta wasu shugabannin Nijar

Daga ofishin jakadancin Amurka an sanar da ‘yan jarida soke taron manema labaran da ya kamata tawwagar Moly Phee ta gudanar a karshen wannan rangadi, to sai dai ba a fadi dalilin daukan wannan mataki ba yayin da a bangaren hukumomin na Nijar aka bayyana cewa su jira sanarwar karshen zama daga ma’aikatar harakokin waje.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Tawagar Jami'an Gwamnatin Amurka Da Ta Kai Ziyara Nijar Ta Fara Tattauna Batun Dimokradiya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG