Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Dakatar Da Burkina Faso Daga Dukan Ayyukanta Sakamakon Juyin Mulkin Da Sojoji Suka Yi

Lieutenant Colonel Paul-Henri Damiba

Kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Burkina Faso daga dukkan ayyukanta, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi ne a makon jiya, har sai an maido da tsarin mulkin kasar, in ji AU a yau Litinin.

Tuni dai aka dakatar da Burkina Faso daga kungiyar hadin kan kasashen Yammacin Afirka, wato kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ko da yake kungiyar ECOWAS ta dakata dora mata takunkumi ba bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Roch Kabore a ranar 24 ga watan Janairu.

A ranar Litinin ne tawagar ECOWAS tare da wakilin Majalisar Dinkin Duniya suka ziyarci Burkina Faso domin ganawa da shugabannin da suka yi juyin mulki kafin yanke shawara kan mataki na gaba.

ECOWAS

Kungiyar ta AU ta dakatar da wasu kasashe biyu na Yammacin Afirka, Mali da Guinea, bayan da sojoji suka kwace mulki a bara. Juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso shi ne na hudu a yankin cikin watanni 18.

Kungiyar ECOWAS da kawayenta na kasa da kasa sun yi Allah-wadai da juyin mulkin, wanda suke fargabar zai iya kara dagula zaman lafiyar kasar da ke fama da tashe-tashen hankula na mayakan Islama.

Jagoran juyin mulkin Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul-Henri Damiba, a makon da ya gabata ya ce kasar za ta koma bin tsarin mulkin da zarar lamura sun daidaitu.

-Reuters