Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaukaciyar Guguwa Ta Kashe Mutane A Madagascar, Mozambique Da Malawi


Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa

Mahaukaciyar guguwar ta kashe akalla mutum 34 a Madagascar, biyu a Mozambique hudu a Malawi, yayin da wasu dubbai suka rasa matsugunansu.

Malawi, wacce ita ma ta yi asarar wutar lantarki na tsawon kwanaki biyu, ta tura tawagar bincike da ceto domin taimakawa mutanen da ake fargabar sun makale a yankunan da ambaliyar ruwa ta mamaye.

Emily Mateyu na cikin dubban mutane a kudancin Malawi da suka rasa matsuguni sakamakon ruwan sama mai kama da bakin kwarya da kuma ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwar Ana wacce ta auku a Malawi a ranar Lahadin da ta gabata.

Mateyu tana barci ne a gidanta da ke gundumar Chikwawa a kudancin Malawi lokacin da ambaliyar ruwa daga guguwar ruwan Ana ta iso.

“Lamarin ya faru da karfe 11 na dare ne. Ambaliyar ruwan ne daga kogin da ke kusa da ya kewaye gidana ya tashe ni. Cikin daren na gudu tare da da na zuwa wani tudu, na baro dukkan dukiyoyina a jike a cikin ruwa.

Ta kara da cewa, “Ba mu da wurin kwana. Har ma cocin da makarantun suma suna cikin ruwa. Abin da muka fi bukata a yanzu shi ne abinci da tufafi domin amabliyar ta mamamaye mana dukiyoyinmu.” In ji Mateyu.

Ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, lamarin da ya tilasta wa mutanen da ke ciki neman mafaka a coci-coci da makarantu.

Chipiliro Khamula mai magana da yawun Ma'aikatar Bala'i da Gudanarwa a Malawi ya ce har yanzu sashen na kan samun rahoton tantancewa daga gundumomin.

Khamula bai tantance adadin mutanen da abin ya shafa.

“A yanzu haka muna samun rahotanni daga kansiloli. Chikwawa kadai tana da gidaje sama da 10,000 da suka yi gudun hijira. Kuma Mwanza yana da sama da mutane 4,000 da abin ya shafa,” in ji shi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG