Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata ‘Yar Gudun Hijira Ta Haifi ‘Ya’ya Uku Lokacin Da Ta Tsere


Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru
Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru

Fatime Eliane wata mata mai dauke da juna biyu ta yi tafiyar kwanaki uku da kafa a watan da ya gabata don gujewa tashin hankalin da ke faruwa a arewacin Kamaru tsakanin makiyaya, manoma da masunta.

Amma da ta isa Chadi ta sake tarar da wani abun damuwa dake jiran ta. Bayan makonni uku, Fatime mai shekaru 32, kuma mahaifiyar yara bakwai, ta haifi 'ya'ya uku a wani asibiti a N'Djamena babban birnin kasar.

Ta ce ko da nake dauke da cikin ban yi tsammanin ‘ya’ya ukuba ne, amma daina yi ta fama da rashin lafiya.

Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru
Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru

Fatime ta ce, ta tsere ta yi gudun hijira daga ƙauyenta Mousgoum da ake sana’ar kamun kifi da noma awatan da ya gabata ,lokacin da makiyayan Larabawa da ake kira Choa, suka far ma kauyen suka kona gidajen makwabta.

Fiye da 'yan Kamaru 100,000 ne suka tsere daga rikicin inda aka kashe mutane da dama a hare-haren ramuwar gayya, wanda ya barke bayan takaddama kan raguwar albarkatun ruwa, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR.

‘Yan Ukun Da Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru Ta Haifa
‘Yan Ukun Da Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru Ta Haifa

Eliane, ta bar mijinta da manyan ’ya’yansu uku a Kamaru, inda suka nemi mafaka a wani wurin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.

A halin da ake cikin yanzu a kasar Chadi, Fatime tana da wadanda za ta ciyar da su bakwai daga dan abincin kadan da ake bai wa 'yan gudun hijira.

Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru Da ‘Yan Ukun Da Ta Haifa
Fatime Eliane Wata ‘Yan Gudun Hijira Daga Kamaru Da ‘Yan Ukun Da Ta Haifa

Surikarta Mariam Abakar ta ce “duk da haihuwar 'ya'yan uku albarka ne, amma akwai matukar damuwa saboda ba mu da abinci ko kudi.”

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG