Yajin aikin wanda shine na farko a bana ya biyo bayan watsewar baram-baram din da aka yi a taron da ya hada shugbannin kungiyoyin malaman makaranta da mambobin kwamitin kula da sha’anin ilimia jiya Lahadi.
Malaman dake wannan yajin aiki sun hada da na frimari da na sakandari sakamakon wasu dadaddun bukatun da suke neman a biya masu,
A hirar shi da Muryar Amurka, sakataren kungiyar Synace ta malaman kwantaragi Mounkaila Halidou ya bayyana cewa, albashi na ma’aikaci ne ba na gwamnati ba ,soboda haka suna da izinin yin abinda suke so da shi.
Wannan mataki na jingine aiki wata hanya ce da malamai ke son amfani da ita don shugaban kasa Mohamed Bazoum ya gane yadda wasu jami’ai ke sakaci da alkawuran da ya dauka ayayin ganawarsa ta kwanakin baya da masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi.
La’akari da cewa yajin aikin malaman makarantun gwamnati abu ne da ya fi shafar karatun ‘yayan talakawa musamman a kasar da kashi 80 daga cikin 100 na malamai ‘yan kwantaragi ne , ya sa kungiyar uwayen yara dalibai APEEN jan hankulan bangarori akan bukatar yin sulhu.
To amma Shugaban ma’aikata a ofishin ministan ilimi Malan Achana Hima ya jaddada cewa a yanzu haka bangarorin na cikin tattaunawa don nemo bakin zare.
Fannin ilimi na kan gaba a jerin ayyukan da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya yi alkawarin baiwa fifiko a tsawon wa’adin mulkinsa kamar yadda ya ayyana a jawabinsa na rantsuwar kama aiki domin a cewarsa ci gaban kasa ba zai samu ba sai da ilimi.
To sai dai rashin jituwa tsakanin malamai da jami’an gwamnati na iya yiwa kudirin shugaban tarnaki.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: