Shekarun wadanda aka ci zarafin nasu na tsakanin 8 da 75, a cewar rahoton binciken Majalisar Dinkin Duniya, inda kungiyar rsf da kawarta ta Larabawa masu dauke da makamai suka aikata galibin fyaden da aka yi a wani yunkuri na tsoratarwa da hukunta mutanen da suke zargin suna da alaka da abokan gabarsu.
“Yawan rahotannin fyaden da muka tattara a Sudan nada tarin yawa,” a cewar shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar, Muhammad Chande Othman, a cikin sanarwar data biyo bayan wani rahoto mai shafi 80 daya kunshi tattaunawa da mutanen da aka ci zarafinsu da iyalansu da kuma shaidun gani da ido.
Rahoton ya bibiyi binciken da kamfanin dillancin labarai na Reuters da kungiyoyin kare hakki suka gudanar akan yawaitar cin zarafi ta hanyar lalata a rikicin na Sudan.
Kungiyar rsf dake yakar rundunar sojin Sudan, ba tayi gaggawar yin martani ga bukatar tofa albarkacin bakinta ba. A baya ta taba cewar za ta binciki zarge-zargen tare da hukunta wadanda suka aikatasu.
-Reuters