Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Babban Asibitin Birnin Al-Fashir Na Sudan Sakamakon Harin Dakarun RSF - Kungiyar Agaji


Sojojin bataliyan na arewacin Sudan a garin Karima, Mayu 19, 2024.
Sojojin bataliyan na arewacin Sudan a garin Karima, Mayu 19, 2024.

Dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari babban asibitin da ke birnin Al-Fashir na Sudan kuma an dakatar da ayyuka a asibitin, abin da kungiyar likitocin agaji ta Doctors Without Borders (MSF) wacce ke tallafa wa asibitin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters kenan a ranar Lahadi

WASHINGTON, D. C. - Birnin, wanda ke yankin Darfur a arewa maso yammacin Sudan, mazauni ne ga mutane fiye da miliyan 1.8 da kuma wadanda suka rasa matsugunansu, kuma yanzu shi ne filin daga na baya baya a yakin da ake gwabza tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, wanda aka fara a watan Afrilun 2023.

Dakarun rundunar RSF, da suka mamaye Khartoum babban birnin kasar da kuma yawancin yankin yammacin Sudan, suna kokarin ci gaba da kutsawa a tsakiyar yankin, yayin da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka ce al'ummar Sudan na tattare da hadarin fadawa kangin yunwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane 130,000 ne suka tsere daga gidajensu a al-Fashir sakamakon fadan da aka yi a watannin Afrilu da Mayu.

Rundunar RSF dai ba ta amsa bukatar yin bayani akan batun ba.

Asibitin da ke kudancin yankin shi ne kadai asibiti a birnin al-Fashir da ke iya kula da majinyata da yawa da ake samu a duk rana sakamakon rikicin, a cewar kungiyar likitocin MSF.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG