Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nemi Dakarun RSF Na Sudan Su Janye Daga Babban Birnin Dafur


Kungiyar Rapid Support Forces (RSF), Sudan
Kungiyar Rapid Support Forces (RSF), Sudan

A ranar Alhamis kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya zarta da kudurin da ya nemi dakarun kar ta kwana na Sudan da su gaggauta daina kawanyar da su ke yi a babban birni daya tilo a yankin Arewacin Dafur da ba ta da iko da shi, kuma wurin da aka ruwaito cewa mutane sama da miliyan suka fake.

WASHINGTON, D. C. - Kudurin da Birtaniya ta gabatar, wanda ya samu amincewa da kuri’u 14 inda Rasha ta kaurace masa, ya kuma yi kira ga rundunar sojin RSF da dakarun Sudan da su hanzarta kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu don a kai ga karshen yakin da suka shafe sama da shekara daya suna gwabzawa.

Kudurin ya bayyana matukar damuwa kan yadda rikicin ya bazu, da kuma sahihan rahotanni da suka ce, rundunar RSF na haddasa tashe tashen hankulla masu nasaba da kabilanci a El Fasher babban birnin Arewacin Dafur, da kuma El Geneina da ke kudancin Dafur a bara.

Jakadiyar Birtaniya a majalisar dinkin duniya, Barbara Woodward ta shaida wa kwamitin a bayan kada kuri’ar cewa, kudurin ya aika da sako mai karfi, wanda ya bayyana cewa ya zama wajibi dakarun RSF su gaggauta dakatar da kawanyar da su ke a garin El Fasher.

Wood ta yi gargadin cewa, kai hari a kan birnin zai yi muni matuka ga mutane miliyan daya da dubu dari biyar da ke zaune a birnin. Ta kuma ce dole ne a kawo karshen mummunan fadan.

A tsakiyar watan Afirilu na shekarar 2023 ne Sudan ta fada cikin rikici, a lokacin da dadaddiyar 'yar tsama tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF ta yi sanadin barkewar rikici a babban birnin Khartoum, rikicin ya kuma bazu zuwa sauran sassa da suka hada da Dafur. Majalisar dinkin duniya ta ce sama da mutane 14,000 ne aka kashe, wasu 33,000 kuma suka jikkata.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG