Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fararen Hula Na Cikin Mawuyacin Hali A Sudan – Kungiyar Likitoci Ta MSF


Doctors Without Borders-Medecins Sans Frontieres
Doctors Without Borders-Medecins Sans Frontieres

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa Medecins Sans Frontieres (Doctors Without Borders - MSF) ta ce fararen hula a Sudan suna fuskantar munanan tashe-tashen hankula a cikin sama da shekara guda da aka kwashe an gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun sa-kai masu adawa da juna.

A yau ranar Litinin MSF ta ce fararen hula suna fuskantar hare-hare da cin zarafi da daga bangarorin biyu.

‘Yan Sudan (Mohammad Ghannam/MSF/Handout via Reuters)
‘Yan Sudan (Mohammad Ghannam/MSF/Handout via Reuters)

MSF a cikin wani rahoto ta ce, raunuka da ake jiwa jama’a da tashin hankali da suke ciki ya kara tsananta sakamakon rugujewar tsarin kiwon lafiya da kuma rashin ba da agajin jin -kai na kasa da kasa.

Ta kara ce, tawagoginta sun yi jinyar dubban mutane da suka jikkata a yaki a yankunan da tashin bama-bamai ya shafa, da harsasai kan gidajen zama da muhimman ababen more rayuwa.

Rikicin Sudan
Rikicin Sudan

A duk fadin kasar Sudan, hanyoyin da jama'a ke samun kulawar ceton rai sun yi matukar lalacewa saboda karancin abinci, cikas da kuma sace-sacen kayayyakin jinya, rashin tsaro da hare-haren da ake kai wa majinyata da ma'aikatan lafiya, da kuma lalata kayayyakin kiwon lafiya.

Ta kuma zargi bangarorin da ke gaba da juna, Dakarun Sojin Sudan (SAF) da kuma na sa-kai (RSF), da "rashin kulawa" da rayuwar dan adam da dokokin kasa da kasa.

Ba a dai samu ji daga kowane bangare ba nan take don yin tsokacin wadannan zarge-zarge.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG