Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya Zai Kada Kuri'a Kan Dakatar Da Kai Hare Hare A Birnin Al-Fashir Da Ke Sudan


MDD
MDD

Ta yiwu ranar Alhamis kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan wani kuduri da Birtaniyya ta gabatar da daftarinsa.

Kudurin dai ya bukaci dakarun RSF su dakatar da hare-haren da suke kai wa a birnin al-Fashir a yankin Dafur a arewacin Sudan, a cewar jami'an diflomasiyya a ranar Laraba.

Daftarin kudurin, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani, ya kuma yi kira da a dakatar da fadan da ake yi a ciki da wajen birnin ba tare da bata lokaci ba, tare da janye dukkan mayakan da ke barazana ga tsaro da lafiyar farar hula.

Biritaniya ta bukaci kwamitin mai mambobi 15 ya kada kuri'a akan daftarin a ranar Alhamis da rana. Dama zartar da kuduri a kwamitin na bukatar akalla kuri'u 9 da suka amince da shi, ba tare da Rasha, China, Amurka, Birtaniya ko Faransa sun yi watsi da shi ba.

A cikin watan Afrilun 2023 ne dai yaki ya barke a kasar Sudan tsakanin sojojin Sudan (SAF) da kuma dakarun rundunar RSF, lamarin da ya haifar da tashin hankalin gudun hijira mafi girma da aka gani a duniya.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG