Sabon labari shi ne irin matakan zahiri da 'yansanda ko jami'an tsaro daban daban suke dauka na maganace matsalar.
Saboda dakile matsalar ya sa kwana kwanan nan babban sifeton 'yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase ya yiwa wasu kwamishanonin kudancin kasar sauyin wuraren aiki ciki har da na jihohin Legas da Ogun.
Malam Bello Yola wani mazauni Legas ne wanda a kwanan nan ya tsallake rijiya da baya a hannun 'yan fashi da makami duk da matakan da hukumomi ke ikirarin dauka saboda dakile matsalar.
Malam Bello Yola yace da ranar Allah aka tareshi tare da abokinsa aka yi masu kwacen kudadensu da wayoyinsu. Yace idan ba'a dauki kwararan matakai ba Legas zata koma a matsayin yadda take da can lokacin da ake tsoronta sabili da tabarbarewar tsaro da kwace, sata da kassara mutane inda ake kashesu a bakin titi.
Sabon kwamishanan 'yansandan Legas yace zasu mayarda hankali akan dakile aukuwar muggan ayyukan ne. Zasu yi anfani da bayanan siri daga jami'ansu kuma kamar yadda babban sifeton 'yansandan Najeriya ya bada umurni, zasu tashi tsaye domin magance natsalar.
Ga rahoton Babangida Jibril.
Your browser doesn’t support HTML5