Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Shirya Su Yaki Masu Tada Kayar Baya-inji Majo Janar Muazu


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Kwamandan runduna ta biyu ta sojojin Najeriya Manjo Janar Sani Muazu yace sojojin kasar sun shirya su yaki masu tada kayar baya

Manjo Janar Sani Muazu ya furta hakan ne lokacin da yake bude taron injiniyoyin sojojin Najeriya a birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo.

Taron na kwana daya an shiryashi ne domin injiniyoyin sojojin kasar su kara damara wajen yaki da masu tada kayar baya a yankin arewacin kasar, musamman arewa maso gabashi.

Janar Muazu yace dole ne sojojin su ci nasarar yakin da suke yi a arewa maso gabashin kasar. Yace kokarin da injiniyoyin ke yi ya kusa ya kawo karshen yakin. Yace fiye da kowane lokaci a halin yanzu aka fi bukatar injiniyoyin.

Kwamandan ya bukaci 'yan Najeriya da su taimakawa askarawan game da yakin da suke yi ba wai a bar sojoji kadai da yakin ba. Yace ya kamata jama'a su taimakawa sojoji da bayanai ko kuma su taimaka da bayanan mabuyar masu tada kayar bayan..

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:01 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG