Sanarwar hana barace barace da tallace tallace ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar ne Tunji Bello.
Yace dokar ba sabuwa ba ce illa dai an kara jaddadata kamar yadda wasu gwamnatocin baya suka kafa.
Dokar zata shafi masu nakasa ne dake barace barace a titunan birnin Legas lamarin da ya sa shugabnnin nakasassu bayyana rashin jin dadinsu da matakan hukumomin na hana barace barace a can baya da kuma yanzu.
Sarkin kutaren Legas Alhaji Ado Na Ahmadu ya bayyana rashin jin dadin nasu. Yace yanzu abun ya zama wani iri. Ba ana yi ba ne domin gyara ba. Ana yi ne don kudi. Yace kwanakin baya an kama kusan mutane biyar amma da aka biya kudin beli an sakesu. Saboda haka dokar ba wai don hana bara ba ne amma don son kai da neman kudi. Wanda yake da kudi sai ya tanada koda za'a kamashi ya biya kana ya cigaba da yin bara.
Shi sarkin kutaren yace yayi shekaru fiye da goma sha biyar bai fita yawon bara ba. Kullum yana zaune a kofar gidansa. Yace wasu basa zuwa bara a waje.
Sani Galadiman guragu matashi ne kuma nakasasshe amma ya rungumi sana'ar yi a birnin Legas domin kaucewa takurawar hukumomi da kuma dogaro ga kai. Yanzu dai yana gudanar da sana'ar daukan hoto. Yace ya duba ya ga ya kamata ya samu sana'ar da ya rike a hannunsa domin dogara ga bara ba hanyar fita ba ce. Yace ya kama sana'ar yin hoto kuma Allah ya bashi shiga a sana'ar. Yana fatan wasu nakasassu zasu canza su rungumi yin sana'a. Yin sana'a zai kawo ma nakasassu sauki ainun.
Ga rahoton Babangida Jibril.