Kotun koli a Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayyar daga aiwatar da shirin daina karbar tsoffin kudi.
A ranar 10 ga watan nan na Fabrairu wa’adin da babban bankin kasar na CBN ya ayyana ya kamata ya fara aiki.
Sai dai yayin wani zama da ta yi a ranar Laraba, kotun kolin kasar mai alkalai bakwai, ta dakatar da shirin daina amfani da tsoffin kudaden har sai an kammala sauraren shari’ar.
A ranar Litinin jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar da kara a kotun inda suka kalubalanci sabon wa’adin, wanda zai kare a ranar Juma’ar mai zuwa.
Tun da farko a ranar 31 ga watan Janairu babban bankin na CBN ya ce za a daina amfani da tsoffin takardun kudin naira 200, 500 da 1000.
Amma bayan korafe-korafe da aka yi ta yi, bankin ya kara kwanaki goma bayan sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari.
Gabanin shigar da karar a kotu, gwamnonin jam’iyyar APC sun kai wa shugaba Buhari ziyara a fadarsa, inda suka nemi a kara wa’adin.
Ko da yake, ba su samu biyan bukata ba, amma shugaban na Najeriya ya ce za a shawo kan matsalar karancin kudaden cikin kwanaki bakwai.
A halin da ake ciki, kotun ta ba bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kudade a kasar umarni da su ci gaba da amfani da tsoffin kudaden har sai kotun ta yanke hukunci a zaman da za ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Tun a watan Nuwambar bara, Najeriya ta soma fitar da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali, sai dai karancin su ya jefa al’umar kasar cikin halin kakani-kayi.
Mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Malam Baba Yusuf, ya ce hukuncin na kotun kolin ya zo a daidai lokacin da ya kamata ganin irin halin kakani-kayi da kudurin na babban bankin kasar ya sanya daukacin ‘yan Najeriya.
Barrista Mainasara Kogo, fitaccen lauya dake da kwarewa a fannin kundin tsarin mulkin Najeriya ya kuma bayyana cewa kotun koli ta yi abun da zai zama dadadde a tarihin kasar yana mai cewa kotun ta nuna muradin talaka yana cikin shari’a ne.
Haka kuma gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara wanda ke cikin gwamnonin uku da suka shigar da karar a gaban kotun koli ya yi marhaba da hukuncin kotun yana mai cewa sun dauki mataki ne don saukakewa talakawan Najeriya gabadaya.
Duk kokarin ji ta bakin babban bankin Najeriya a yayin hada wannan rahoto ya ci tura.
Saurari cikakken rahoto daga Halima AbdulRauf:
Your browser doesn’t support HTML5