Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ya Tura Wakilai 30,000 Don Taimakawa Wajen Sauya Tsofin Kudade


Babban bankin Najeriya ta CBN
Babban bankin Najeriya ta CBN

Babban Bankin Najeriya ya ajiye wakilai 30,000 a wurare daban-daban a duk fadin kasar don taimakawa marasa galihu da wadanda ke zaune a lungu da sako don musanyar kudadensu da sabon kudin kasar.

Bankin ya kuma kara wa'adin musayar tsofaffin kudade da kwanaki 10, yana mai cewa kusan kashi 30 cikin 100 na tsofaffin kudaden na ci gaba da yaduwa. Sai dai masu sukar lamirin sun ce kamata ya yi hukumomi su dage kan wa'adin canjin kudin.

Aikewa da jami’an babban bankin Najeriya CBN ya biyo bayan sanarwar da aka bayar a ranar Lahadin da ta gabata na tsawaita wa’adin kwanaki 10 na wa’adin ranar 31 ga watan Janairu ga ‘yan kasar da su musanya tsohon kudadensu da sabon kudin.

Babban bankin ya ce an yi hakan ne don bai wa ‘yan kasa damar musanya tsofaffin takardun kudi da kuma rage asara, musamman ga wadanda ke yankunan karkara a kudin Najeriya da ke da karancin hanyoyin samun kudaden shiga.

Babban bankin na CBN ya kuma amince da wa’adin kwanaki bakwai bayan sabon wa’adin, wanda ya zama tilas ga ‘yan kasar da har yanzu ke rike da tsohon kudin su kai wa babban bankin kasar.

Sai dai yayin da wasu da dama ke yabawa da karin lokaci da aka samu, wani mazaunin Abuja Prince Eromosele ya ce CBN ya ba da gari ne domin matsin lamba daga bangaren siyasa.

"Ina jin cewa an tsawaita wa'adin ne saboda martanin da 'yan takarar shugaban kasa na APC da PDP suka yi," inji Eromosele. Ina matukar takaici da gwamnan CBN. Tun da aka tsayar da ranar talatin da daya, kamata ya yi a bar shi a haka. ‘Yan Najeriya sun riga sun fara daidaitawa da shi, in har mu ka tsara dokoki, sai mu bi su.”

An kaddamar da sake fasalin takardun kudin Najeriya 200, 500, da kuma naira 1000 a watan Oktoba ne.

An tsara matakin ne da nufin yaki da jabun kudaden, da karfafa karin kudade ta yanar gizo da kuma rage aikata laifuka, ciki har da yadda ake sayen kuri’u ta hanyar amfani da tarin kudaden da aka tara.

Ndu Nwokolo, wani babban mai hadin gwiwa ne a cibiyar nazarin tsare-tsaren jama'a ta Nextier, ya ce musayar kudaden na da fa'ida.

“Ina ganin abin da CBN ya yi shi ne duba wasu sauye-sauyen masu muhimmanci ga sha'anin kudi, bisa la’akari da yanayin da kasar ke ciki a yanzu.” Ya ce, “Kuna da zabe a gaban ku, ga matsin lamba daga jam’iyyun siyasa, kana ga matsalar man fetur, wadannan abubuwa duk sun taka rawa a halin da ke ciki. Don haka, ina ganin sun kalli lamarin ne gaba dayansa."

Kusan kashi 40 cikin 100 na 'yan Najeriya basu da damar samun banki. Nwokolo ya ce musanyawar wata dama ce ta gyara hakan.

Babban bankin dai ya sha sukar lamiri daga masu adawa ga sauya kudin, ciki har da wasu 'yan majalisar dokokin kasar.

A makon da ya gabata ne kakakin majalisar ya yi barazanar damke gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele, kan kin bayyana a gaban kwamitin majalisar da ke binciken zargin karancin kudaden Naira da aka sake musu fasali a fadin kasar.

A halin da ake ciki rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya na binciken Emefiele bisa zarginsa da aikata laifuffukan kudi, da bayar da tallafi ga ayyukan ta’addanci da kuma tafka almundahana.

Wannan ne karon farko da Najeriya ta sabunta kudin kasar cikin kusan shekaru ashirin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG