Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu bankunan ‘yan kasuwa a kasar za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi.
Bankunan sun dauki wannan mataki ne don ba jama’a damar su sauya tsoffin kudadensu yayin da wa’adin kammala amfani da su yake karatowa.
Babban bankin Najeriya na CBN ya ba da wa’adin 31 ga watan Janairu a matsayin ranar da za’a dena amfani da tsoffin kudaden.
A karshen watan Nuwambar bara, CBN ya kaddamar da sabbin kudaden takardun naira na 200, 500 da 1000 wadanda aka sauyawa masu fasali.
A tsakiyar makon nan mai karewa, bankin na CBN ya ce ba zai tsawaita wa’adin karbar tsoffin kudaden ba, lamarin da haifar da korafe-korafe daga jama’a.
Majalisar wakilan Najeriya ta nemi gwamnan bankin Godwin Emefiele da ya tsaiwata wa’adin zuwa 31 ga watan Yulin bana, amma abin ya ci tura.
A cewar Emefiele, wa’adin kwanaki 100 da aka ba jama’a ya ishe su su shigar da tsoffin kudadensu a bankuna.
Majalisar ta wakilai ta aikewa da Emefiele wasikar gayyata don ya bayyana gabanta, amma gwamnan babban bankin na Najeriya ya ki amsa gayyata inda ya ba da wasu uzurori da ke gabansa.
A zaman da ta yi a ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya yi barazanar zai sa ‘yan sanda su kama Emefiele idan bai bayyana gaban majalisar a ranar Talata mai zuwa ba.
A halin da ake ciki, bankunan First Bank da Guaranty Trust da wasu bankunan ‘yan kasuwa sun ba da sanarwar cewa za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi domin mutane su mika tsoffin kudaden da ke hannunsu.