Koriya ta Arewa Ta Ce A Shirye Ta Ke Ta Tattauna Da Amurka Kan Wargaza Shirin Nukiliyarta

Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

Tun can farko shugaban Amurka ya ce zai gana da shugaban Koriya ta Arewa idan ya amince ya wargaza shirinsa na mallakar makaman nukiliya da a baya ya rantse babu wanda zai hana kasarsa mallakarsu

A shirye kasar Korea ta Arewa ta ke, ta tattaunawa da Amurka a kan wargaza shirinta na makaman nukiliya, a cewar wani baban jami’in Amurka a jiya Lahadi.


Wannan itace babbar alamar dake nuna shugaban Korea ta Arewar Kim Jong Un ya kuduri aniyar ganawa da shugaba Donald Trump, tun bayan lokacin da ita Korea ta Arewar ta gabatar da shawarar gudanar da taron koli a watan da ya gabata.
Trump ya fada cewar yana so ya gana da Kim kafin karshen watan Mayu. Sai dai babu wani karin bayani a kan abubuwan da za a tattaunawa akai da kuma inda za a yi tattaunawar.


Amma kuma jami’an Amurka sun ce akwai tuntubar sirri tsakanin Wasshington da Pyongyang.
A baya, Korea ta Arewa tayi alkwarin dakatar da shirin nukiliyarta bisa yarjejeniyar musayar a bata taimakon abinci da kuma dage mata takunkumin tattalin arziki. Sai dai sau tari Korea ta Arewa tana karya alkawuranta.