‘Yan kasar Koriya ta Kudu na cigaba da bayyana kwarin guywarsu akan yiwuwar cimma yarjejeniyar zaman lafiya biyo bayan shawarar ban mamaki da shugaba Donald Trump ya yanke, ta amincewa ya gana da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un don warware takaddamar da ake yi akan makaman nukiliya a mashigen Koriya.
“Babu wanda ke fatan yaki, ba Koriya ta arewa ba, ko Koriya ta kudu, ko ma kasashen dake kewaye da su. Don haka ina gani za a sami nasarar cimma zaman lafiya,” a cewar wani mazaunin birnin Seoul Jang Soon-ae yau Talata.
Fiye da kashi 70 na mutanen da suka bayyana ra’ayoyinsu a kuri’ar jin ra’ayin da aka kada kwanan nan na goyon bayan taron kolin da ake sa-ran yi tsakanin Kim da shugaban Koriya ta kudu Moon Jae-in a watan Afirilu, da kuma wanda za a yi a watan Mayu tsakanin Kim da Trump.
A watan Nuwamban shekarar 2017, Koriya ta arewa ta dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya da masu linzame masu tsanani da ta kwashe shekaru biyu tana yi, gwaje-gwajen da suka maida hankali akan kirkirar makami masu linzame, masu cin dogon zango da zasu auna ciki-cikin Amurka.
Facebook Forum