A yau Alhamis shugaban kasar koriya ta Arewa da ta Kudu zasu gana da juna a lokacin wani taro tsakanin jakadun kasashen biyu a wani kauye mai suna Panmunjonm, dake a yankin nan da ba soja a cikinsa wanda ya raba kasashen biyu tun yakin basasar da suka yi da juna tsakanin shekarar 1950 zuwa 1953.
Shuwagabannin Kasashen biyu dai sau biyu kawai suka taba haduwa da juna tun bayan rabuwarsu, daya a shekarar 2000 da na karshen a shekarar 2007.
An cimma Yarjejeniyar yin wannan taro tsakanin kasashen 2 bayan ziyarar ba-zatan da Kim Jong Un, ya kai zuwa kasar China, tafiyar shi ta farko zuwa kasashen waje tun lokacin da ya anshi mulki a shekarar 2011 bayan rasuwar mahaifinshi Kim Jong na biyu. Kasar China ta ce Kim, ya yarda da shirin dakatar da kokarinsa na neman makaman nukliya a yankin.
Facebook Forum