Korea ta Arewa ta amince ta zauna da makwabciyarta Korea ta Kudu a mako mai zuwa, domin a tsara yadda za a yi wani taron koli tsakanin kasashen biyu a watan Afrilu mai zuwa.
Korea ta Kudu ce ta sanar da wannan shiri a yau Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa, ko wanne bangare zai aika da wakilai uku-uku a ranar Alhamis, zuwa kauyen Panmunjom da ke kan iyakar kasashen biyu.
Ri Son Gwon, shi ne zai kasance jam’in da zai jagorancin tawagar Korea ta Arewa a wajen wannan tattaunawa, sannan Cho Myoung-gyon ya jagoranci tawagar Korea ta Kudu.
Taron kolin da za a yi a watan na Afrilu tsakanin shugabannin kasashen biyu, wato Moon- Jae-in da kuma Kim Jong Un na Korea ta Arewa, na zuwa ne, bayan hadin kan da kasashen biyu suka yi a karkashin tuta guda domin karawa a gasar Olympics da aka kammala a Korea ta Kudu a kwanan nan.
Har ila yau, taron na zuwa ne, gabanin wata ganawa da za a yi ta gaba-da-gaba, tsakanin shugaban Amurka, Donald Trump da kuma Kim Jong Un.
Ana sa ran za a yi zaman ne a watan Mayu, domin tattaunawa kan shirin dakile gina makamin nukiliya da Korea ta Arewan ke yi.
Facebook Forum