Tace bayan da ayyukan ta'adanci ke kara yawaita a kasashen ukku shugabannin sun kuduri yin damarar yaki da 'yan ta'ada a kasashensu ba tare da bata wani lokaci ba..
Kasashen sun kuduri kafa rundunar hadin gwuiwa domin yakar 'yan ta'ada. Rundunar ce aka dankawa wuka da nama a yankunan kasashensu domin a kawar da 'yan ta'ada. Kungiyar tace tana kan bakanta na goyon bayan matakan da kasashen sahel suka dauka domin yaki da 'yan ta'adan.
Sun kara sanarwa cewa kungiyar na goyon bayan kungiyar dake fafatawa da 'yan ta'ada.
Taron na birnin Yammai ya bukaci skatariyar taron da ta hanzarta wurin shigo da kayan aiki ba tare da bata lokci ba saboda an dukufa da aiki gadan gadan.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
.