Shugaba Jammeh, wanda yayi jawabin kaddamarda dokar ta-bacin jiya ana saura kwannaki biyu kafin wa’adin mulkinsa ya cika, yana ci gaba da fuskantar baranar zama “saniyar ware”, bayanda ministocinsa da dama suka ajiye aiki.
Ministocin da suka yi watsi da aiyukkan su a baya-bayan nan sun hada da ministocin kudi, harakokin waje, ciniki da kuma yanayi.
A halin yanzu, ita kuma jam’iyyar sabon shugaba, Adama Barrow, ta fito da sanarwa dake jan kunnen ma’aikatan tsaron Gambia da cewa duk wanda bai hanzarta chanja biyayyarsa zuwa ga Adama Barrow ba, za’a yi mishi daukar “dan tawaye ne kawai.