Dangane da haka ne shugaban na Mauritania ya gana da shugaban Gambia mai barin gado, Yahya Jammeh sannan ya wuce Senegal inda ya sadu da Adama Barrow, mutumin da ya kada Jammeh a zabe, wanda kuma a yau ake shirin rantsarda shi a matsayin sabon shugaban Gambia a birnin Banjul.
Sai dai kuma shugaba Aziz ya gayawa manema labarai cewa karfin imaninsa na cewa za’a warware wannan rikici cikin lumana ya soma raguwa ainun.
A halin yanzu kuma...Dakarun Najeriya da Senegal yanzu haka suna bakin iyakar kasar Gambia, inda suka lashi takobin ganin sai sun fatattaki shugaba Yayah Jammeh muddin yaci gaba da yin kunnen kashi na kiran da shugabannin kasashen Yammacin Afrika suka yi masa na ya sauka daga kan karagar mulki domin mikawa zababben shugaba Adama Barrow wanda ya lashezaben na daya ga watan Disambar bara.
Rahotanni sunce yanzu haka dai mutanen Gambia da dama suna ci gaba da arcewa zuwa zuwa kasar ta Senegal.