Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Gambiya Yayi Alkawarin Kafa Gwamnati Mai Adalci


Sabon Shugaban Gambiya Adama Barrow
Sabon Shugaban Gambiya Adama Barrow

Sabon Shugaban Gambiya Adama Barrow ya ce zai kafa kwamitin tabbatar da gaskiya da sake sasanta jama'a, don nazarin zarge-zargen mulkin danniya a zamanin tsohon Shugaba Yahaya Jammeh na tsawon shekaru 22.

"Shekaru 22 lokaci ne mai tsawo," a cewar Barrow a wata hira da Muryar Amurka. Ya kara da cewa, "Jama'a na bukatar sanin gaskiya."

Wani mai baiwa Barrow shawara ya gaya ma manema labarai jiya Litini cewa kafin ya bar kasar ranar Asabar, Jammeh ya sace dala miliyan 11 daga asusun gwamnati, ya kuma kwashe motocin alatu ta jirgin sama.

A baya kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam sun zargI shi Yahya Jammeh da take hakkin dan Adam a mulkinsa mai, ciki har jefa masu adawa da shi a siyasance da kuma 'yan jarida gidan yari.

Jammeh ya fice daga Gambiya ranar Asabar ne sanadiyyar barazanar matakin soji daga kungiyar kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS. Da dai tsohon Shugaban ya ki ne ya amince da nasarar da Barrow ya yi a zaben Shugaban kasa na ran 1 ga watan Disamban bara.

Sabon Shugaban ya ce ya ki rokon da Jammeh ya yi na a bar shi ya cigaba da zama a Gambia, saboda ba zai iya tabbatar da tsaron lafiyar Jammeh ba.

Barrow, dan shekaru 51 da haihuwa, ya ce gwamnatinsa za ta dukufa wajen ganin an yi cikakken gyara ga tsarin zaben kasar, ta yadda za a kayyade wa'adin shugaban kasa nan gaba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG