Amma babban alkalin kotun kolin kasar Mr. Emmanuel Fagbule ya ki ya amince da bukatar Yahya Jammeh na cewa ya hana rantsar da Adama Barrow a matsayin shugaban kasar gobe Alhamis.
Matsayin da alkalin alkalan ya dauka ya sake jefa Yahya Jammeh cikin rudani.
Shi dai shugaba Jammeh yayi hayar alkalai daga kasashen Najeriya da Saliyo domin cika ka'idar kotun kolin kasar saboda su saurari karar da ya gabatar akan zaben. Saidai babban alkalin kasar Justice Fagbule yace alkalan ba zasu samu zuwa ba.
Kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka sau biyu tana aikawa da tawaga mai karfi a karkashin shugaban Najeriya Muhammad Buhari.
Inji Malama Shehu Garba kakakin shugaban Najeriya suna fata Yahya Jammeh da mutanen kasar Gambia zasu bi dokar kasarsu da abun da tsarin mulki yace a yi.
Takaddamar siyasa dake faruwa yanzu ya sa kasar ta dauki zafi har 'yan kasar sun fara ficewa domin gudun abun da ka biyo baya, inji Malam Garba Shehu.
Yayinda da kakakin shugaban Najeriya ke rokon 'yan Gambia su rungumi zaman lafiya shi kuwa kakakin shugaban kasar Senegal, kasar da ta kewaye Gambia cewa yayi daga gobe Yahya Jammeh ya zama tsohon shugaban kasa.
Dr. Saidu Ahmed Dukawa na jami'ar Bayero dake Kano yace babu dadi a ce a wannan karni wani shugaba ya ki mika mulki bayan ya fadi zabe. Amma kuma babu dadi a yi anfani da karfin soja. A cigaba da matsin lamba ta siyasa ciki da waje har ya saduda ya sauka.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.