Yau Alhamis ne ya kamata a rantsar da shi a babban birnin kasar Banjul.
Shugaban Mauritania Ould Abdel Aziz ya tattauna da Jammeh a jiya Laraba kafin ya zarce zuwa Senegal inda ya gana da Barrow.
Yace ba zan iya tabbatar da abin da zai faru a Gambia idan na fita daga cikinta. Yakamata in kasance a nan don in ci gaba da tuntubar yan uwana yan Gambia.
Yace ba zan iya kare rashin zuwana Gambia a wannan mawuyacin lokacin ba. Tilas ne inzo in yi shawara da ‘yan uwana al’ummar kasar Gambia. Na tattauna da ‘dan uwana shugaba Jammeh, yanzu bani da kwarin gwiwa. Amma zamu nemi hanyar lumana ta warware matsalar da zata dace da al’ummar Gamba, da kuma kowa.
Rundunar kasashe ECOWAS tana zaman ko ta kwana a kan iyakar Gambia da Senegal tana jiran umarni kai mamaya idan Jammeh ya ki sauka mulki.
Babban hafsan sojojin kasar Gambia Ousman Badjie ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa jiya Laraba cewa, jami’ansa ba zasu nunawa dakarun kasashen Afrika tirjiya ba idan suka ketara iyaka.