Inji Malam Haruna da yayi magana yace shi bai san dalilin da ya sa Adama Barrow da aka ce ya ci zabe ya soma babatu da bakinsa ba har ma yana yiwa shugaban dake kan gado barazana.
Yace me ya sa bai yi hakuri ba har sai ya karbi mulki kafin ya fara cewa zai kai Yahya Jammeh kotun kasa da kasa domin a yi masa hukumci akan zargin cin zarafin wasu 'yan kasar Gambia? Yace rashin hankali ne yayi lamarin da ya tsoratar da Yahya Jammeh ya dauki matakin da ya dauka.
To amma yace Yahya Jammeh nada gaskiya lokacin da yace a sake zaben idan an kadashi magana ta kare. Yace to a je a sake zaben idan Barrow ya sake ci babu wata hujja kuma.
Sun kira kungiyar ECOWAS kada tayi anfani da karfi. Ta nemi hanyar lafiya ta kawo sulhu. Kamata yayi su samar masa mafaka inda zai je shi kuma Barrow ya dare kan mulki.
Sun yi na'am da shawarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar. Ya yiwa Yahya Jammeh tayin zuwa zama a Najeriya idan yana son yin hakan.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.