AGADEZ, NIGER - Binciken ya ce gubar na da matukar illa ga muhalli sannan kuma tana da matukar illa ga lafiyar jama’a da kuma ruwan shansu, wanda tuni dai lamarin ya tayar da hankulan kungiyoyin dake kare muhalli.
Rahoton binciken na zuwa ne kasa da shekaru biyu bayan da kanfanin na Cominak ya rufe hakar karfen uranium a Arlit dake cikin Jihar Agadas a Arewacin Nijar inda tsofaffin ma’aikata suka shigar da kara a gaban wata kotun kasar Faransa dake birnin Paris kan irin illar da gubar ta yiwa ma’aikata dake da nasaba da aikin hako uranium.
Binciken ya ce gubar nada matukar illa ga muhalli da kuma lafiyar jama’a lamarin da ya tayar da kungiyoyin kare muhalli.
Fiye da shekaru hamsin kanfanin na Cominak ya shafe yana aikin hako karfe uranium a Arlit abinda ya sa mazauna garin da wasu tsofaffin ma’aika basu mamakin jin abinda rahoton ya bayyana.
Shi dai kanfanin na Cominak na daga cikin cibiyoyin hakar karfen uranuim da kanfanin Orano na kasar Faransa ya mallaka a Agadas dake Arewacin Nijar kuma ya dakatar da aikinsa ne a cikin watan Maris din shekara ta 2021, sai dai kanfanin na Cominak ya bayyana cewa ta bakin manajan kanfanin Faruk Assalek sun mutunta dukkanin ka’idodin da aka shinfida musu.
Ya ce acin aiki kamar lokacin da muka fara tsabatace muhalli ana kulawa da lafiyar jama’a da ayukan tsabatace muhalli kama daga ruwan sha da iska da kuma gandun daji zamu cigaba da kulawa dasu a sanin mu tsawan lokacin da muka shafe anan muna mutunta dokokin da aka shinfida ta fuskar fitar da guba.
Acikin watan da ya gabata ne kungiyar tsofaffin ma’aikata ta sakem aka kanfanin na Cominak a gaban kotun ma’aikata dake birnin Yamai saboda rashin cika alkawuran da suka daukar musu.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Your browser doesn’t support HTML5