Gwamnatin kasar ce ta shirya wannan haduwa da nufin samar da tsari ta yadda nan gaba maniyata za su sauke farali cikin kyakkyawan yanayi, saboda haka Fira Minista da mahalarta taron su bullo da shawarwarin da za su taimaka a sami mafita.
Damfarar maniyata da yawaitar kafuwar kamfanonin wakilai ko agent na daga cikin matsalolin da ke haifar da dambarwa a Nijer a kowacce shekara idan lokacin tafiya kasar Saudiya ya zagayo, dalili kenan gwamnatin kasar ta shirya wannan taro da ya hada jami’an gwamnati da na hukumar alhazzai da shugabanin kamfanonin agent da wakilan kamfanonin jiragen sama, don zakulo hanyoyin mafita.
Rashin mutunta jaddawalin dakon alhazai kamar yadda aka tsara tun tashin farko, wata matsala ce da ke rikita dukkan abubuwan da aka tsara na sha’anin haji daga Nijar, amma wakilin kamfanin jiragen Max Air Boukari Sani Zilly na alakanta faruwar abin da yanayin da ake ciki a Nijer.
Sabon tsarin rajistar maniyata ta yanar gizo System GAHO da hukumomin saudiya suka shimfida a baya, bayan nan wata matsala da agent ke cewa ta zo ta karu akan wadanda suka dabaibaye lamura. Dalili kenan ya sa sashen Hausa ya nemi jin martanin hukumar alahazzai ta kasa wato COHO.
A jawabin bude taro fira minista Ouhoumoudou Mahamadou ya gargadi bangarori su maida dukkan wasu bambance bambance wuri daya don ganin an bullo da shawarwarin da za su taimaka a kawo karshen irin matsalolin da ke jefa maniyatan Nijer, cikin halin tashin hankali a kowace shekara idan lokacin haji ya zagayo.
Za a kamala wannan taro a ranar Talata 31 ga watan Janairu mai karewa.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.