Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Kasar Nijar Sun Fara Yajin Aiki Na Wuni Biyu 


Yajin Aikin Ma'aikata a Nijar
Yajin Aikin Ma'aikata a Nijar

Yau ma’aikatan kasar Jamhuriyar Nijar suka fara yajin aikin wuni biyu da  nufin nuna rashin jin dadi a game da abinda suka kira saba alkawarin da hukumomi suka yi dangane da wasu tarin bukatun da suka gabatar.

NIAMEY, NIGER - To sai dai uwar kungiyar kwadago ta CDTN ta ce wannan yajin aiki bai shafi ma’aikatanta ba.

Yajin aikin, wanda ya biyo bayan rashin gamsuwa da abubuwan da aka tsayar bayan wata ganawar da ta hada shugaban kasa Mohamed Bazoum da shugabanin kungiyoyin kwadago mambobin ITN da na kungiyar CDTN a makon jiya kawancen ITN wato CNT USTN USPT da CGSL ne suka kira shi don tayar da mahukunta daga barci inji Mounkaila Halidou babban sakataren uwar kungiyar kwadago ta CNT.

A cewarsa magoya bayan wadannan kungiyoyi sun amsa kira a ko ina a sassan Nijar a wuni na farko na wannan yajin aiki.

A daya bangare an cimma yarjejeniya a tsakanin CDTN da gwamnati a farkon makon nan sakamakon biyan bukatun da shugabanin kungiyar suka ce sun samu a karshen wannan zama saboda haka wannan yajin aiki bai shafi magoya bayanta CDTN ba inji sakataren tsare tsare Mahamadou Mansour Adamou.

A jajibirin barazanar yajin aikin da suka yi shugaba Mohamed Bazoum ya gayyaci shugabanin kungiyoyin kwadago a fadarsa inda ya yi alkawalin shafe hawayen ma’aikata dangane da wasu matsalolin da suka addabe su haka kuma kungiyoyin sun ci gaba da tantaunawa da ministan kwadago a karshen mako sai dai rashin gamsuwa ya sa suka yanke shawarar shiga wannan yajin aiki koda yake CDTN ba ta yajin aikin ba saboda yarjejeniyar da suka cimma da hukumomi abinda ke fayyace rarrabuwar kan da ke tsakanin ma’aikata a wannan kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Ma’aikatan Kasar Nijar Sun Fara Yajin Aiki Na Wuni Biyu .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG