NIAMEY, NIGER - Haka kuma ‘yan sandan sun gabatar da wasu gaggan ‘yan fashi da makami cikinsu har da wani jami’in tsaro da aka kora daga aiki saboda aikata babban laifi.
Gungun farko na mutanen da sashin binciken ‘yan sandan farin kaya ya rutsa da su na kunshe da wasu ‘yan damfara kimanin 12 ‘yan asalin kasashen Afrika ta Yamma da na Afrika ta tsakiya.
Wadanan mutane da ke amfani da hanyoyin sadarwa na zamani wajen shirya gadar zare sun damfari kudade sama da million 300 na cfa da sunan odar kayan yaji da zuma. Kamar yadda kakakin hukumar ‘yan sandan Commissaire Principal Dr. Abou Mountari ya bayyana a taron manema labari.
Haka kuma ‘yan sandan na PJ sun yi nasarar kama wasu mutane biyar da suka dauki lokaci mai tsawo suna hana wa mazauna birnin Yamai barci inda su kan bi dare wajen fasa manyan shaguna ko kai farmaki a gidaje mutane tare da hadin bakin wani tsohon jami’in tsaro da ke amfani da kakinsa don badda sahu.
Alkali mai shigar da kara a babbar kotun Yamai Chaibou Moussa wanda ya ziyarci ofishin na ‘yan sandan PJ don gane wa idanunsa ‘yan takifen da aka kama, ya jinjina wa ‘yan sanda da nasarar wannan aiki.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: