SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da gamayyar rundunar jami'an tsaro a Sakkwato ta ce ta kama makamai a hannun wasu magoya bayan wata jam'iyya kuma tana sane da shirin da wata jam'iyya ke yi na daukar fansa akan zargin da take yi.
Gamayyar rundunar jami’an tsaro a jihar ta Sokoto domin tabbatar da zaman lafiya a zabukan 2023, ta ce ta sami wasu bayanan tsaro na sirri na yunkurin jan daga tsakanin manyan jam’iyun jihar na APC da PDP masu hamayya da juna.
Jam'iyyun na APC da PDP na kokarin ramuwar gayya ne bisa zargin da su ke wa junansu na hana zaɓe a wasu runfunan zaɓe sama da 300 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalissar ƙasa a makon jiya.
Shugaban gamayyar jami’an tsaron kuma kwamishinan ‘ƴan sandan Jihar ta Sokoto Muhammad Hussaini Gumel ya ce dole su taka wa wannan yunkurin birki gabanin zaben da lokacin da kuma bayan zaben gwamnonin da ake tunkara a ranar 11 ga wannan watan na Maris.
Haka kuma Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa, tun bayan kammala wancan zaben, gamayyar rundunar tsaron wadda ta kumshi wakilan dukkan hukumomin tsaro ta ke zagaye da sintiri a cikin babban birnin Jihar domin nunawa jama'a shirinsu.
Masu sharhi akan lamurran yau da kullum na kallon wannan yunkurin da ‘yan siyasa ke yi a zaman abin kunya ga kasa irin Najeriya, wadda ke cike da matsalolin rayuwa kamar yadda Farfesa Bello Badah ke gani.
Ko bayan wannan yunkurin na amfani da karfi da jami'an tsaro suka ce sun gano, da yawa magoya bayan jam'iyyu sun fara tarewa wuraren ibadah suna addu’o’i don samun nasarar jam'iyyunsu.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5