KANO, NIGERIA - Da yammacin jiya Talata ne Jami’an rundunar suka kama ‘dan majalisar wanda ke wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a majalisar wakilan Najeriya, bisa tuhumar sa da hannu wajen tarzomar da ta wakana a ranar Litinin a garin Tudun Wada dake yankin kudancin Kano.
Rahotannin daga majiyoyin hukumomi tsaro a Kano sunce kimanin mutane uku ne suka mutu kuma da dama suka jikkata bayan da tarzoma ta barke a tsakanin magoya bayan Jam’iyyun APC da NNPP a garin na Tudun Wada.
Alhassan Ado Doguwa daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar majalisar wakilan Najeriy daga mazabar Tudun Wada da Doguwa kuma shine hukumar zabe ta INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya ce yanzu haka ‘dan majalisar wakilan na sashin binciken kisan kai da sauran manyan laifuka na rundunar dake Bompai kuma jami’ai na ci gaba da yi masa tambayoyi domin tattara bayanai, kana daga bisani su girfanar da shi a gaban kuliya.
Yanzu haka dai al’ummar Jihar Kano sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan mataki na ‘yan sanda, inda wasu kamar Rabiu Ahmad da Abdulhadi Abubakar ke cewa, matakin na ‘yan sandan yayi la’akari da yadda aka dade ana zargin dan majalisa Alhassan Ado da irin wadannan laifuka kuma gashi ana tunkarar zaben gwamnonin kasa nan da makonni uku masu zuwa.
A nasu banagaren, masana dokoki da harkokin shari’a a Najeriya sun ce bincike da kuma gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifuka na cikin ayyukan da doka ta rataya a wuyan ‘yan sanda, kamar yadda Farfesa Nasiru Adamu Aliyu SAN malami a tsangayar koyar da aikin lauya ta Jami’ar Bayero ya bayyana.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da majalisar dokokin Najeriya ke kokarin tabbatar da dokar da zata kafa hukuma ta musamman da za ta tabbatar da hukunci akan masu aikata laifukan zabe, kamar yadda yake kunshe cikin sabuwar dokar zabe ta kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari: