Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: An Gano Wasu Kalubalolin Tsaro Game Da Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisa


IGP Alkali Baba Usman
IGP Alkali Baba Usman

Sa’o’I kafin zaben shugaban kasa na 2023 a Najeriya da aka dade ana jiran gani, Sufeto Janar ‘Yan sandan Najeriya, Usman Baba ya ce har iyau ayyukan ‘yan ta’adda, masu fashin daji da haramtacciyar kungiyar rajin kafa Biafra ta IPOB da reshen ‘yan bindiganta ESN, na ci gaba da zama babban kalubale.

Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriyan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labara a birnin tarayya Abuja a jiya Juma’a.

Ya kuma ce ayyukan ‘yan bangar siyasa da rigingimun cikin gida da na tsakanin jami’iyyu su ma suna zama kalubale ga zaben na yau 25 ga watan Fabrairu 2023.

Ya ce karuwan kai hare-hare a kan gine-ginen hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da masu kutse da masu adawa da tsarin dimokaradiyya ke kaiwa, shi ma yana ci gaba da zaman babban kalubale.

Baba ya ce ba za a amincewa kungiyoyin tsaron kamar su rundunar Amotekun a kudu maso yamma da Ebubeagu a kudu maso gabas ko kuma Benue Guards su yi aiki a zaben na yau Asabar ba.

“A halin da ake ciki kuma, na bada umarni cewa babu irin wadannan kungiyoyin tsaro da zasu yi aikin tsaro ga harkokin siyasa,” in ji Sufeton ‘yan sandan.

Ya kuma jaddada aniyar ‘yan sanda na ganin an gudanar da zaben da daskiya da kuma adalci, yana mai cewa an jibge jami’an tsaro 425,106 da zasu kula da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da ake gudanarwa yau Asabar.

Da yake lissafo kalubaloli da ‘yan sanda ke fuskanta kafin babban zaben kasar, Baba ya ce, “Duk da cewa ‘yan sandan Najeriya sun kammala shiri na tabbatar da zabe cikin lumana, an gano wadannan a matsayin kalubaloli da ka iya addabar zaben.”

“Wadannan matsalolin suna tare damu kuma zamu ci gaba da dakile su. A kokarin ganin mun dakile wadannan matsalolin, mun kara kaimi a ayyukan mu kana mun yi imanin cewa lamurra sun inganta fiye da lokuta da suka shude.

XS
SM
MD
LG